‘Yar Nijeriya Ta Farko Da Ta Fara Tuka Jirgi Mai Sukar Ungulu Na Yaki Ta Mutu

‘Yar Nijeriya Ta Farko Da Ta Fara Tuka Jirgi Mai Sukar Ungulu Na Yaki Ta Mutu

Daga Comr Abba Sani Pantami

Rundunar sojin sama ta Nijeriya ta sanar da mutuwar matukiyar jirgin sama Tolulope Arotile sakamakon hadarin mota a Kaduna.

Sanarwar da kakakin rundunar Ibikunle Daramola ya fitar ta ce Arotile ita ce mace ta farko da ta fara tuka helikwaftan yaƙi a Nijeriya wacce aka kaddamar a watan Satumban 2017.

Sanarwar ta ce matukiyar ta rasu ne a jiya Talata bayan gamuwa da hadarin mota inda ta samu munanan raunika a Kaduna.

Marigayiyar wace ƴar asalin jihar Kogi ce, an bayyana cewa ta bayar da gudunmuwa sosai a yaki da ƴan bindiga masu fashin daji a jihar Neja inda ita ce ke tuka jiragen rundunar Gama Aiki.

Babban hafsan sojin sama na Nijeriya Air Marshal Sadique Abubakar ya ce mutuwar jami’ar babban rashi ga rundunar tare da jajantawa iyalanta a madadin dukkanin jami’an rundunar sojin sama na Nijeriya.

About admin 155 Articles
About Us AREWA COOL MUSIC specializes itself in the online promotional and online magazine in aspect of upcoming urban releases in africa. We established ourselves, within the online community, in order to offer musicians, record labels, and managers our continuous experience, skills, and expertise that we have in the digital realm of music marketing. Our marketing campaigns use strategic methods which are set in place to effectively maximize exposure, build brand awareness, as well as creating a grassroots movement.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*